27 Nuwamba 2021 - 11:56
Sojojin HKI Sun Kama Wasu Falasdinawa Guda 3

Rahotanni da muka samu daga yankin Falasdinu dun bayyana cewa sojojin HKI sun kai samame a garin Kafr Al-labad da kuma sansanin falsdinawa yan gudun hijira a Diyashe kuma sun cafke wasu falasdinawa guda 3 babu laifin fari balle baki.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Wani rahoto da da kamfanin dillacin labarai na Wafa ya watsa ya nuna cewa a ranar talata da ta gabata ma sojojin HKi sun kai samame a yankuna daban daban dake gabar yammacin kogin Jodan kuma sun kama fasladinawa akalla guda 17.

Gwamnatin Yahudawan Sahyuniya ta mamaye gabar yammacin kogin Jodan da birnin Qudus babban birnin Falasdinu tun a shekara ta 1967.

Wasu masu tsattsauran ra’ayin a Isra’ila da suka hada da Fira ministan Isra’ila Naftali Bennett suna kallon yankunan dake gabar yammacin kogin jodan dake bangaren falasdinu a matsayin cibiyar tarihin yahudawa.

342/